Gwamna Ya Dauki Ma’aikata 424 Domin Inganta fannin Kiwon Lafiya
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da daukar sabbin ma’aikatan lafiya 424 a fadin jihar, a matakin da zai taimaka wajen inganta kiwon lafiya. Wannan daukar ma’aikatan ya hada da ungozoma 205 da kwararru 219 daga bangarorin lafiya daban-daban.A cikin sanarwar da Daraktan Yada Labaran Gwamna Buni, Mamman Mohammed, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa za a rarraba ma'aikatan zuwa yankunan karkara da birane domin tabbatar da ingantacciyar kula da lafiya ga jama’a. Wannan shiri na daukar ma’aikata ya fito ne daga bukatar cike gibin da ke akwai a fannin kiwon lafiya a jihar.Mai Mala Buni ya yi alkawarin ci gaba da inganta harkar lafiya a jihar ta hanyar samar da kayan aiki da ma’aikata masu kwarewa. Hakan na daga cikin manyan manufofin gwamnatin sa na inganta jin dadin al'umma.Gwamnan ya ...








