Tinubu Ya Yaba wa Ganduje akan kwarewar sa a siyasa
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta 75, inda ya yaba da gudunmawar Ganduje ga ci gaban ƙasa da jihar Kano. Tinubu ya bayyana cewa Ganduje ya taka muhimmiyar rawa a matsayin shugaban jam’iyyar APC, yana ƙarfafa haɗin kai da cimma nasarorin siyasa.
A cikin sakon murnar, Tinubu ya jinjina wa Ganduje bisa jajircewarsa da kokarin da ya yi wajen inganta harkokin siyasa a jihar Kano da Najeriya baki ɗaya. Shugaban ya yi addu'a ga Ganduje, yana fatan samun lafiya da farin ciki a rayuwarsa.
Tinubu ya bayyana cewa, nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a ƙarƙashin jagorancin Ganduje sun ƙara inganta haɗin kai a cikin jam’iyyar. Ya gode wa Ganduje bisa shawarwarin siyasa da goyon bayan da ya bayar a lokuta da dama, yana ƙarf...








