Zargin Damfara: APC Ta Dakatar Da Ɗan Takarar Ƙaramar Hukuma A Legas

Jam’iyyar APC a jihar Legas ta dakatar da ɗan takararta na shugaban ƙaramar hukumar Eti-Osa ta Gabas, Samad Ogunbo, bisa zargin karɓar albashi daga wurare biyu na gwamnati a lokaci guda.

Rahotanni sun bayyana cewa Ogunbo na karɓar albashi daga hukumar SUBEB da kuma matsayinsa na mai sanya ido kan harkokin lafiya a ƙaramar hukumar tun a shekarar 2022.

Hukumar SUBEB ta bayyana cewa ba ta san Ogunbo na riƙe da wani muƙami a ƙaramar hukumar ba, kuma hakan ya saɓa wa dokokin aikin gwamnati a jihar Legas.

Bayan samun korafi game da wannan al’amari, jam’iyyar APC ta cire sunan Ogunbo daga cikin jerin ‘yan takarar da za su tsaya takarar shugabancin ƙaramar hukumar.

Majiyoyi sun ce an ɗauki wannan matakin ne saboda zargin yaudarar gwamnati da karya dokar aikin gwamnati da Ogunbo ya yi.

A wani labarin kuma, ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere ta bayyana goyon bayanta ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ya kammala shekaru takwas a mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *