Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Yin Hattara: Tsohon Shugaban Majalisa Ya Jaddada Illar Talauci a Arewa

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana damuwarsa kan matsalar yunwa da talauci a Najeriya, musamman a yankin Arewa. A yayin raba tallafin hatsi da kayan abinci ga talakawa a mazabarsa ta Yobe, ya ce barin jama’a a cikin yunwa na iya jefa su cikin mawuyacin hali.

Sanata Lawan ya yi kira ga shugabannin siyasa da su nemi hanyoyin magance matsalolin tattalin arziki da tsaro da kasar ke fuskanta. Ya jaddada cewa gwamnati na bukatar tallafin masu ruwa da tsaki wajen rage yunwa da fatara a cikin al’umma.

A cewarsa, wannan tallafi na abinci ba zai warware matsalar yunwa ba, amma yana da matukar mahimmanci a wannan lokaci. Ya kuma yi kira ga duk wanda ke da hali ya taimaka wa wadanda ke cikin bukata, domin yawancin ‘yan Najeriya suna cikin mawuyacin hali na talauci.

Sanata Lawan ya kuma ba da gudummawa domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a jihar Yobe, yana mai nuna cewa wannan na daga cikin al’amuran da ke bukatar kulawa ta musamman.