
Sadiq da Gumsu Abacha, ‘ya’yan marigayi Janar Sani Abacha, sun yi martani kan maganganun da tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya yi game da mahaifinsu. A cikin martaninsu, sun bayyana cewa tarihi zai tuna da gudunmawar da Sani Abacha ya bayar a matsayin shugaba.
Sadiq Abacha ya kare mahaifinsa a shafinsa na Facebook, inda ya ce, “Duk da sukar da ake yi wa mahaifina, tarihi zai tabbatar da cewa ya kasance shugaba nagari.” Ya kara da cewa, “Mutumin ne da aka yi wa hassada, amma tarihi zai tuna da alherinsa.” Sadiq ya bayyana alfahari da mahaifinsa tare da jaddada cewa, “Lallai kai ne mutumin da suke fatan su zama kamarsa.”
Hakanan, Gumsu Abacha ta yi martani tare da cewa ya kamata mutane su ji tsoron Allah kan abin da suke fada. A cikin sakon ta na X, ta rubuta kalma guda “Weakling,” wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu amfani da shafukan sada zumunta.
Martanin ‘ya’yan Abacha ya zo ne bayan kaddamar da littafin tarihin rayuwar IBB, inda ya bayyana nadamar soke zaben June 12, 1993, tare da zargin Abacha da mukarrabansa na jagorantar wannan hukuncin ba tare da saninsa ba.
Wannan lamari ya jawo hankalin jama’a, inda dangin Abacha ke kare sunan mahaifinsu daga zarge-zargen da ake yi masa a tarihi.