Yan Takarar Gwamna a Ondo Sun Nemi Haɗin Kai da Aiyedatiwa Bayan Nasararsa

Yan takarar gwamna 13 da suka fafata a zaɓen jihar Ondo sun bayyana matsayarsu kan nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa, inda suka ce sun amince da sakamakon zaɓen kuma suna shirin haɗa kai da shi domin gina sabuwar jihar Ondo.

Sun bayyana hakan ne lokacin da suka gana da Aiyedatiwa a ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Akure, babban birnin jihar a ranar Juma’a.

‘Yan takarar sun yi alƙawarin goyon bayan gwamnatin Aiyedatiwa domin ci gaban jihar, sannan suka buƙaci ya dama da sauran jam’iyyun siyasar da suka fafata da shi.

Jam’iyyun da suka halarci taron sun haɗa da Accord (A), AA, APM, NNPP, APP, ADP, ADC, APGA, LP, YP, YPP, BP da ZLP.

Gwamna Aiyedatiwa ya yabawa ‘yan takarar da shugabannin jam’iyyunsu kan alƙawarin da suka yi na marawa gwamnatinsa baya, inda ya ce ba zai yi wasa da goyon bayansu ba.

Ya bayyana cewa ci gaban jihar abu ne wanda ya zama wajibi kan kowa da kowa don haka ya buƙaci masu ruwa da tsaki su zo a haɗa kai domin cimma wannan manufar.

.