
Jami’an rundunar ‘yan sanda a jihohin Abia da Nasarawa sun gudanar da babban samame kan ‘yan bindiga, wanda ya haifar da musayar wuta mai zafi. A yayin wannan aikin, ‘yan sandan sun hallaka ‘yan bindiga guda bakwai tare da ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya tabbatar da wannan nasara a cikin wata sanarwa da ya fitar. A cewarsa, an yi musayar wuta ne a lokacin da jami’an tsaron suka kai samame kan maɓoyar masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Osisioma, jihar Abia, bayan samun bayanai na sirri.
A yayin samamen, ‘yan sandan sun ƙwato makamai guda biyu na ƙirar AK-47, jigida guda shida, da harsasai guda 34. Jami’in ya bayyana cewa an kai mutanen da aka ceto asibiti domin samun kulawa.
“Jami’an hukumar ‘yan sandan Najeriya sun sake samun gagarumar nasara wajen dakile garkuwa da mutane da kuma hana aikata miyagun laifuka,” in ji ACP Adejobi.
A jihar Nasarawa, rundunar ‘yan sandan tare da haɗin gwiwar sojojin Najeriya sun kashe wani sanannen mai garkuwa da mutane, Abdullahi, wanda aka fi sani da ‘Honor’, a wani sumame da aka kai a Akwanga. Wannan mutum yana cikin jerin wadanda hukumomi ke nema saboda aikata laifuka da dama.
Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya jinjinawa jami’an bisa ga ƙwazon da suka nuna a wajen gudanar da wannan samame. Wannan gagarumar nasara ta kara tabbatar da niyyar jami’an tsaro na yaki da ‘yan bindiga a Najeriya.