‘Yan Sanda Sun Fadi Masu Hannu Wajen Tayar da Bama Bamai a Zamfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da tashin ababen fashewa a wasu ƙauyukan jihar, inda ta zargi ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Lakurawa da laifin dasa bama-baman.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Muhammad Shehu Dalijan, ya bayyana cewa an samu fashewar bam a ƙauyen Yar Tasha da ke kan hanyar Dansadau, wanda ya janyo mutuwar mutum ɗaya tare da raunata wasu uku. CP Dalijan ya ce, “Mai motar ya taka wani bam da aka dasa a ƙarƙashin gada, wanda ya haifar da fashewar.”

Binciken farko ya nuna cewa ragowar ‘yan ta’addan Lakurawa ne suka dasa bama-bamin bayan sun fuskanci matsin lamba daga jami’an tsaro. CP Dalijan ya ce, “A halin yanzu, ‘yan ta’addan na ƙoƙarin gano hanyar zuwa dajin Birnin-Gwari ta cikin jihar Zamfara.”

Hakanan, dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma sun hallaka ‘yan ta’adda masu yawa a jihar Zamfara bayan sun karɓi kiran gaggawa daga mutanen gari da ‘yan banga a ƙauyen Yar Galadima.

Wannan lamari ya jawo hankalin al’umma game da matsalar tsaro a jihar, inda ake fuskantar ƙarin hare-hare daga ‘yan ta’adda. Rundunar ‘yan sandan ta ƙara tabbatar da cewa tana aiki tukuru domin tabbatar da tsaro a duk fadin jihar.

Ana sa ran cewa jami’an tsaro za su ƙara kaimi wajen yaki da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifi a yankin, tare da taimakon al’umma wajen samar da bayanai masu amfani.