
A wani gagarumin samame, rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta dakile wani hari da ‘yan bindiga suka kai kan wata motar haya a karamar hukumar Jibia. Hare-haren sun faru ne a ranar 24 ga Disamba da misalin karfe 8:30 na dare, inda ‘yan bindigar suka yi yunkurin sace fasinjoji goma.
Bayan samun kiran gaggawa, DPO na Jibia ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa wurin. Sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar, inda jami’an tsaro suka samu nasarar ceto dukkanin fasinjojin goman. Duk da haka, mutum hudu daga cikin wadanda aka ceto sun samu raunuka daga harbin bindiga, kuma an garzaya da su asibiti don samun kulawa.
Sai dai, rahotanni sun bayyana cewa mutum biyu daga cikin wadanda suka ji rauni sun mutu a asibiti yayin da ake kokarin ceto rayukansu. Wannan lamarin ya jefa al’umma cikin damuwa da jimami.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa tana ci gaba da kokarin kamo ‘yan bindigar da suka tsere, tare da gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin. CP Aliyu Abubakar Musa ya yabawa jaruntakar jami’an tsaro, yana mai kira ga jama’a da su rika bayar da rahoton duk wani abu da suka zargi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.