
A jihar Kano, rundunar ‘yan sanda ta cafke wasu jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) guda biyu bisa zargin harbe wata yarinya mai suna Patient Samuel, wacce ta mutu a unguwar Jaba Quarters. Wannan lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba, 5 ga watan Maris 2025, lokacin da jami’an NDLEA suka yi amfani da bindiga a wani abu da har yanzu ba a tantance ba.
Majiyoyi sun bayyana cewa, bayan harbin, an dauki yarinyar zuwa asibitin koyarwa na Abdullahi Wase, inda aka tabbatar da rasuwarta. Jami’an NDLEA da aka kama sun hada da Nass Ridwan Usman, mai shekara 23, da Sna Ismaila Yakubu, mai shekara 26, wadanda ke aiki a hedkwatar hukumar a Kano.
A yayin bincike, ‘yan sanda sun gano kayayyaki a hannunsu, ciki har da babur ɗin aiki, harsashi ɗaya, da harsasai guda huɗu masu kaurin 7.62×51mm. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cafke jami’an NDLEA, yana mai cewa suna gudanar da bincike don gano gaskiyar lamarin.
Kakakin NDLEA na jihar Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ya ce suna gudanar da bincike kan lamarin, inda ya tabbatar da cewa za su fitar da sanarwa bayan sun gama gano gaskiyar abin da ya faru. Wannan lamari ya jawo hankalin al’umma game da tsaro da kuma yadda hukumomi ke gudanar da ayyukansu a jihar Kano.