
ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ƴan ta’addan Lakurawa sun bayyana a jihar Zamfara. Matawalle ya ƙaryata waɗannan ikirarin, yana mai jaddada cewa a halin yanzu babu ƴan ta’addan Lakurawa a cikin jihar ko ma a jihar Kebbi da ke makwabtaka da ita.
Matawalle ya bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar fatattakar ƴan Lakurawa zuwa ƙasarsu ta Mali. Ya ce wannan matakin na sojoji ya ba da damar tabbatar da tsaro a yankin, kuma akwai kyakkyawar hulɗa tsakanin dakarun Najeriya da na ƙasar Mali.
A yayin jawabin sa ga manema labarai a Gusau, Matawalle ya ce: “Babu ƴan Lakurawa a kowane yanki na wannan ƙasa, ba ma a jihar Zamfara ko Kebbi ba.” Wannan bayani na Matawalle ya zo ne a lokacin da wasu rahotanni suka bayyana cewa ƴan Lakurawa ne ke da alhakin dasa bama-baman da suka hallaka wasu mutane a jihar.
Shugaban hukumar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu Dalijan, ya tabbatar da cewa ƴan Lakurawa sun kasance a cikin jihar a kwanakin baya, amma Matawalle ya musanta hakan, yana mai cewa sojoji sun tilasta musu komawa ƙasarsu.
Hakan ya jaddada cewa gwamnatin jihar na ci gaba da kokarin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a Zamfara, tare da shirin kawo karshen ta’addanci a wannan yanki. Matawalle ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta umarci sojoji da su kawo ƙarshen ta’addancin da ƴan bindiga ke yi a cikin shekarar 2025.