Yan Kwankwasiyya Sun Yi wa Masoyin Atiku Rubdugu kan ‘Sauya Shekar’

Wani malamin jami’a, Dr. Usman Isiyaku, ya fuskanci caccaka daga magoya bayan Rabi’u Musa Kwankwaso bayan ya yi zargin cewa Kwankwaso na yi wa Shugaba Bola Tinubu aiki ta karkashin ƙasa. Wannan ya jawo fushin ƴan Kwankwasiyya, wadanda ke ganin cewa kalaman sa sun zama abin ƙarya ne da rashin gaskiya.

Usman Isiyaku ya caccaki Kwankwaso bisa jinkirin da ya yi wajen bayyana matsayarsa kan dokar ta ɓaci da Tinubu ya kafa a jihar Rivers. Dr. Ibrahim Musa, wanda ke daga cikin ƴan Kwankwasiyya, ya bayyana cewar binciken Isiyaku ba gaskiya bane, yana mai cewa labarinsa ya yi kama da kanzon kurege.

A cikin wannan yanayi, ƴan Kwankwasiyya sun yi tsokaci kan yadda masoyan Atiku Abubakar ke ƙoƙarin dora alhakin rashin nasarar su a kan Kwankwaso. Wannan ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ganin akwai alamar tambaya game da maganganun masanin.

Shugaban NNPP a Kano, Hashimu Dungurawa, ya bayyana cewa Kwankwaso na da dalilin da ya hana shi shiga kawancen jam’iyyu, yana mai jaddada cewa jam’iyyar NNPP za ta ci gaba da tunkarar zaɓen 2027.