
Ƙungiyar matasan Niger Delta (NDYC) ta bayyana adawarta ga ƙudirin haraji da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gabatar, inda suka yi watsi da shi a matsayin wanda zai amfanar da yankuna ƙalilan ne kawai.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, jagoran NDYC, Kwamared Israel Uwejeyan, ya ce ƙudirin yana cike da kura-kurai da zai ƙara tazara tsakanin masu gata da wadanda ke ƙasa. Matasan sun yi kira ga majalisar tarayya da ta yi watsi da wannan ƙudiri, suna mai cewa yana da kyau a kawo tsare-tsare da zasu amfani dukkan ‘yan Najeriya.
Uwejeyan ya ce, “Wannan ƙudirin, wanda aka nuna shi a matsayin mafita ga ƙalubalen ɓangaren kuɗi a Najeriya, yana cike da kura-kurai waɗanda suka fifita wasu yankunan shafaffu da mai, yayin da ya bar wasu musamman yankin Neja Delta a baya.”
Ƙungiyar ta ƙara da cewa an yi amfani da arziƙin da aka samu daga albarkatun noma na Arewa wajen gina muhimman ababen more rayuwa a Kudancin Najeriya, amma yanzu ana kokarin wargaza wannan al’ada ta samun ci gaba.