
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugabannin jam’iyyar APC guda biyar a jihar Zamfara, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gidan Sanata Abdulaziz Yari. Wannan lamari ya faru ne a yayin da shugabannin ke tafiya daga yankin Kaura Namoda ta Kudu zuwa Mafara.
Cikin wadanda aka sace sun hada da Yahaya Sani Dogon Kade, Shugaban Dan Isah Ward, da Bello Dealer, Shugaban Sakajiki Ward, kamar yadda majiyoyi suka tabbatar. Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun kai harin ne a lokacin da shugabannin ke cikin motocinsu.
Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojojin Najeriya ke kokarin murkushe ‘yan ta’adda a yankin, bayan samun nasarar damke wani kasurgumin dan ta’adda, Kachallah Hassan Nabamamu, a makon da ya gabata.
Gwamnatin jihar Zamfara da hukumomin tsaro suna ci gaba da gudanar da bincike kan wannan lamari, tare da kira ga al’umma da su ba da gudummawa wajen samar da bayanai da za su taimaka wajen kamo wadanda suka aikata wannan ta’asa.
Kodayake har yanzu ba a sami sabbin bayanai kan yadda za a kubutar da wadanda aka sace ba, amma al’ummar jihar na fargabar karuwar hare-hare daga ‘yan bindiga a wannan lokaci.