Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Miyetti Allah

A jihar Kwara, yan bindiga sun kai farmaki inda suka hallaka shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Idris Abubakar Sakaina, a daren ranar Asabar, 8 ga watan Maris, 2025. Wannan mummunan lamarin ya faru ne a gaban gidansa da ke Oke Ose, cikin birnin Ilorin.

Alhaji Idris Abubakar Sakaina, mai shekaru 32, an harbe shi a lokacin da yake cikin gidansa, inda rahotanni suka tabbatar da cewa yan bindigan sun tare shi kafin su kai masa wannan hari. Wata majiya ta bayyana cewa bayan kisan, yan bindigan ba su karɓi komai daga wajensa ba, suna barin shi cikin jini.

Wani ganau mai suna Aina’u Sarki ya bayyana cewa ya kasance tare da Sakaina mintuna 20 kafin a kai masa wannan hari, inda wani ya kirasa a waya yana sanar da shi cewa an harbe shugaban.

Hadimin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan hulɗa da al’ummomi, Muhammed Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa suna shirin gudanar da jana’izar marigayin. Haka zalika, rundunar yan sandan jihar Kwara ta fara bincike kan wannan kisan, inda ta yi alkawarin gudanar da bincike mai zurfi don gano wadanda suka aikata wannan mummunan aikin.

Marigayin, wanda tsohon mataimaki ne na shugaban ƙaramar hukumar Moro, ya kasance kuma jagoran matasan Fulani a jihar Kwara. Wannan kisan ya jawo fargaba a cikin al’umma, inda ake kira ga hukumomi suyi duba da tsaro a yankin.