Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Kusam 20 a Jihar Benue

A ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairu 2025, yan bindiga sun kai hari a wasu kauyuka biyu a cikin ƙaramar hukumar Kwande a jihar Benue, inda suka hallaka akalla mutane 19. Wannan sabon harin ya jawo tsoro da firgici a tsakanin mazauna yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa, a cikin harin na farko da aka kai ranar Asabar, manoma 16 suna kan hanyarsu ta komawa gida ne lokacin da aka yi musu kwanton-bauna, inda aka jefar da gawarwakin su a cikin Kogin Katsina-Ala. Wani mazaunin kauyen Mbanduwa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa maharan sun yi wannan mummunar aiki a kan titin Kashimbila.

A wani harin na biyu da aka kai ranar Litinin, an kashe mutane uku a kauyen Boaguwa, inda maharan suka ci gaba da kai farmaki. Wannan ya sa mutane da dama daga yankunan da abin ya shafa suka fara barin gidajensu don neman tsira a Jato Acka.

Shugaban kungiyar Mzough U Tiv Worldwide, Kwamfurola Iorbee Ihagh, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa akwai bukatar a tura karin dakarun soji don shawo kan matsalar tsaro a yankin.

Duk da haka, rundunar ‘yan sandan jihar Benue ba ta bayar da wani bayani kan wannan sabon hari ba, wanda ya kara jawo hankalin hukumomi da al’umma game da matsalar tsaron da ake fuskanta a jihar.