‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Jami’ar Tarayya, Sun Sace Dalibai

A daren Talata, ‘yan bindiga sun kai hari jami’ar Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurdi, jihar Benuwai, inda suka sace wasu dalibai, lamarin da ya jefa sauran daliban cikin firgici. Wani dalibi mai suna Ashar Lubem ya bayyana cewa an sace dalibai hudu daga cikin jami’ar, duk da cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar ta tabbatar da cewa dalibai biyu aka sace.

Bayan faruwar lamarin, daliban jami’ar sun nuna damuwarsu kan rashin jin dadi da tsoron lafiyarsu. Lubem ya ce, “Tun bayan faruwar lamarin, har yanzu ba mu ji labarinsu ba. Dukkan daliban suna cikin tsoro da firgici.”

Wata majiya ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun yi garkuwa da dalibai mata a harabar jami’ar, wanda hakan ya sa daliban suka gudanar da zanga-zanga suna bukatar hukumomi su dauki mataki na gaggawa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, Sewuese Anene, ta ce suna gudanar da bincike kan lamarin, kuma sun fara aikin ceto daliban da aka sace. Wannan hari na zuwa ne a lokacin da al’umma ke fama da matsalolin tsaro a Najeriya, inda ‘yan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a wurare daban-daban, suna barin mutane cikin fargaba da rashin kwanciyar hankali.

Hukumar jami’ar ta nemi daukar matakai na gaggawa don tabbatar da tsaron dalibai da ma’aikatan jami’ar, yayin da ake ci gaba da fatan ganin an ceto daliban da aka sace cikin koshin lafiya.