Yan Adawa Sun Fara Wani Shirin Ture Tinubu a Zaɓen 2027


Jam’iyyar Labour, wacce ta samu nasarar shiga sahun manyan jam’iyyun siyasa a Najeriya, ta fara shirin tunkarar zaɓen 2027. Jam’iyyar ta yi wani taro na musamman domin fara shirin kifar da gwamnatin APC a zaɓen shekarar 2027.

A yayin taron, wanda aka gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya, shugaban tattaro jama’a na jam’iyyar LP, Marcel Ngogbehi ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai sun shiga Aso Rock Villa a 2027.

Ngogbehi ya ce jam’iyyar LP za ta mayar da hankali kan neman goyon bayan yan ƙasa a yanzu, domin samun nasara a zaɓen 2027. Ya ce za su hada kan al’umma, domin samun karɓuwa a sassan Najeriya.

“Mun shirya wannan taron ne domin neman yadda za mu hada kai mu samar da mafita ga matsalolin Najeriya,” in ji Ngogbehi. “Ina kira a gare ku da ku kulla alaka da mutane, ku sanar da su manufar jam’iyyar mu. Idan muka hada kai za mu iya kawo sauyi.”

Jam’iyyar LP ta ce za ta mayar da hankali kan matsalolin hauhawar farashi, rashin tsaro, matsalar lantarki, ilimi da tattalin arziki. Ta ce za ta hada kan yan Najeriya domin kafa gwamnati a 2027.

A wani labarin da jaridar Vanguard ta wallafa, jam’iyyar LP ta ce bangarorin ilimi da tsaro za su samu kulawa idan aka zabe ta a 2027.