
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi kira ga zaman lafiya da hadin kai domin ci gaban jihar da kasa baki daya. A yayin da ya ziyarci fadar Ohinoyin na Ebira, Bello ya bukaci al’ummar jihar Kogi su goyi bayan Gwamna Ahmed Usman Ododo da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Yahaya Bello ya bayyana cewa manufofin Tinubu za su kai Najeriya ga ci gaba mai dorewa idan aka ba shi goyon baya. Tsohon gwamnan ya nemi ‘yan Najeriya su yi hakuri tare da bai wa gwamnatin Tinubu goyon baya domin magance matsalolin da suka hana ci gaban kasar.
Sarkin Ebira, Tijani Ahmed Anaje, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya tare da yin addu’a domin ci gaban Kogi, yana mai kira ga al’ummar yankin su ba Gwamna Ododo goyon baya domin cimma nasarorin da ake bukata.
Yahaya Bello ya yi wannan bayani ne bayan kotun Abuja ta bayar da belin sa, yana mai cewa ya kamata a karfafa gwiwar hadin kan al’umma domin samun ci gaba a jihar Kogi da Najeriya baki daya.