Yahaya Bello Ya Musanta Zargin Karkatar da Naira Biliyan 80

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya musanta zargin da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta ke masa na karkatar da Naira biliyan 80 daga asusun gwamnatin jihar a lokacin mulkinsa.

A wata shari’a da aka gudanar a gaban Mai shari’a Emeka Nwite a babbar kotun tarayya da ke Abuja, Bello ya bayyana cewa ba shi da hannu a cikin wannan tuhuma. EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan kan tuhume-tuhume 19 da suka shafi zamba da wawure kuɗaɗen gwamnati.

A yayin zaman kotun, lauyan EFCC, Kemi Pinheiro, SAN, ya janye bukatar da aka shigar da farko na matso da ranar gurfanar da wanda ake tuhuma, yana mai cewa wannan bukata ta ci karo da abubuwan da suka faru a dangane da shari’ar. Duk da haka, lauyan Yahaya Bello, Joseph Daudu, SAN, bai yi jayayya da wannan mataki ba.

A baya, hukumar EFCC ta bayyana cewa Yahaya Bello ya ki mutunta sammacin da ta aika masa, wanda hakan ya kai ga cafke shi. Wannan shari’a na ci gaba da kasancewa cikin hasashen yadda za a gudanar da ita a gaba.

Wannan lamari ya jawo hankalin jama’a game da yadda hukumomi ke gudanar da bincike kan masu ruwa da tsaki a harkokin gwamnati, musamman ma a fannin cin hanci da rashawa.