
A yau zamu Yi muku bayani yadda Ake yin Istikhara a cikin musulunci, istikhara Wani adduar ne na Neman jagorancin a cikin al’amura. A Musulunci, ana yin istikhara lokacin da mutum ke da shakka ko kuma yana neman shawara kan wani abu mai muhimmanci. Ga yadda ake gudanar da istikhara:
1. Niyyah (Niyya)
– Ka fara da samun niyyar yin istikhara da zuciya. Ka sanar da Allah cewa kana neman shawararsa game da abin da kake son yi.
2. Yayin da ka tayar da Sallah inma na Farilla ko na Nafila bayan an Karan ta Suratul fatiha da ko Wani Sura da kake so sai ka karanta wannan adduar bayan hakan
An karbi daga Jaabir Ibn ‘Abdullaah (Allah ya kara yarda da shi), ya ce: Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya kasance yana umurtar mu da yin addu’ar neman shiriya a cikin dukkan al’amuranmu, kamar yadda yake koyar da mu wata Surah daga cikin Al-Qur’ani. Ya (sallallahu alaihi wa sallam) yana cewa: “Idan ɗayanku yana da niyyar yin wani lamari, to ya yi sallar nafila raka’a biyu, sannan ya yi wannan addu’a…”
اللَّهُمَّ إِنِّي استخيرُكَ بعِلْمِكَ، واستقدِرُكَ بقدرتِكَ، واسألُكَ من فضلِكَ العظيمِ، فإنَّكَ تَقْدِرُ ولا أَقْدِرُ، وتَعْلَمُ ولا أَعْلَمُ، وأنتَ عَلَّامُ الغُيوبِ. اللَّهُمَّ إن كنتَ تعلمُ أنَّ هذا الأمر خيرٌ لي في ديني ومعاشي وعاقبة امري، أو قال عاجل امري وآجله، فاقدُرْه لي ويسِّرْه لي، وإن كنتَ تعلمُ أنَّ هذا الأمر شرٌّ لي في ديني ومعاشي وعاقبة امري، أو قال في عاجل امري وآجله، فاصرفه عني واصرفني عنه، واقدُر لي الخير حيث كان ثم ارضِني.
Allaahumma ‘innee ‘astakheeruka bi’ilmika, wa ‘astaqdiruka biqudratika, wa ‘as’aluka min fadhtikal-‘Adheemi, fa’innaka taqdiru wa laa ‘aqdiru, wa ta’lamu, wa laa ‘a’lamu, wa ‘Anta ‘Allaamul-Ghuyoobi, Allaahumma ‘in kunta ta’lamu ‘anna haadhal-‘amra-[sai a Fadi Al’amarin] Khayrun lee fee deenee wa ma’aashee wa ‘aaqibati ‘amree – [ko ace] ‘Aajilihi wa ‘aajilihi – Faqdurhu lee wa yassirhu lee thumma baarik lee feehi, wa ‘in kunta ta’lamu ‘anna haadhal-‘amra sharrun lee fee deenee wa ma’aashee wa ‘aaqibati ‘amree – [ko ace] ‘Aajilihi wa ‘aajilihi – Fasrifhu ‘annee wasrifnee ‘anhu waqdur liyal-khayra haythu kaana thumma ‘ardhinee bihi.
Ya Allah, ina neman shawarar Ka da Ilimin Ka, kuma ina neman taimakon Ka da Ƙarfin Ikon Ka, kuma ina roƙon Ka da Falalar Ka Mai Girma. Hakika, Kai ne Mai Iko, ni kuma ba ni da iko. Kai ne masani, ni kuma bani da sani, kuma Kai ne Masanin abubuwan da ke boye
Ya Allah, idan Ka san wannan al’amari [a ambaci al’amarin] ya fi alheri a addinina, rayuwata, da lahirata [ko: a duniya da lahira], to Ka ƙaddara mini shi, Ka sauƙaƙa mini shi, sannan Ka yi mini albarka a cikinsa.
Amma idan Ka san cewa wannan al’amari yana da illa a addinina, rayuwata, da lahirata [ko: a duniya da lahira], to Ka nisantar da shi daga gare ni, Ka nisantar da ni daga gare shi, kuma Ka ƙaddara mini alheri a duk inda yake, sannan Ka sanyaya raina da shi.
Za a iya karanta wannan dua bayan sallar farilla ko na nafila.
3. Bari Al’amari ga Allahu SWT
Bayan yin dua, Bawa ya kasance ya bar al’amarin sa ga Allah. Yana Mai yakini cewa Allah zai nuna masa Mafita a cikin wannan Al’amari
Musulmi ya sani cewa Duk wanda ya nemi shawarwarin Ubangiji ba zai yi nadama ba, kuma wanda ya nemi shawarar muminai zai ji nutsuwa a hukuncinsa. Allah ya ce a cikin Al-Qur’ani:
“Ka yi shawara da su a cikin al’amari, sa’an nan idan ka yanke hukunci, sai ka dogara ga Allah.” [Surah Aal Imraan: Ayah 159].