Wuridin ya hayyu ya qayyum

Ya hayyu ya kayyum Suna ne daga cikin Asma’ul Husna, wato sunayen Allah Madaukaki. yana daga cikin sunayen Allah mafi girma, waɗanda ake amfani da su wajen roƙo, neman taimako, da neman sauƙi daga gare Shi.

Al-Hayyu: Shi ne Allah mai rai da bai gushewa, wanda rayuwarsa ba ta da iyaka.

Al-Qayyum: Shi ne mai kula da komai, wanda ba ya bukatar wani abu amma komai da kowa yana bukatarsa

Wannan magana tana nuna cewa Allah ne mai rai, wanda ba ya gushewa, kuma shi ne wanda ke kula da komai da tsare-tsarensa.

Ma’anar “Ya Hayyu Ya Qayyum”


Ya Hayyu yana nufin: Ya Mai Rayuwa dawwamammiya.
Allah ne kadai yake rayuwa har abada, ba ya mutuwa, kuma yana kula da komai cikin iKon sa.

Ya Qayyum yana nufin: Ya Mai Tsayuwa Da Kansa Kuma Mai Tsayar Da Dukkan Halittu.
Allah ne mai kula da komai, yana kiyaye halittu kuma yana cika bukatunsu.

Yadda Ake Yin Wirdin “Ya Hayyu Ya Qayyum”
1. Yin Wirdin Bayan Sallah
Bayan ka kammala sallarka, ka zauna cikin nutsuwa ka yawaita cewa:

“Ya Hayyu Ya Qayyum, bi rahmatika astagheeth.”
Wannan yana nufin:

“Ya Mai Rayuwa dawwamammiya, Ya Mai Kula da Komai, ina neman taimakonKa a cikin rahamarKa.”

2. Karanta Lokacin Damuwa
Idan kana cikin damuwa, ko kana son Allah ya warware maka wata matsala, ka zauna ka yawaita cewa:

Ya Hayyu Ya Qayyum” 100 ko fiye, tare da fatan Allah zai amsa maka.

3. Rokon Taimako Daga Allah
Idan kana neman taimako ko mafita daga wata matsala, ka hada wannan zikirin tare da addu’a kamar haka:

Ya Hayyu Ya Qayyum, Ya Allah, ka sauƙaƙa mini wannan lamari cikin rahamarka da ikonka.”

Anfanin Sa

1. Samun Sauƙi daga Damuwa
Zikiri na Ya Hayyu Ya Qayyum yana sa mutum ya samu nutsuwa, kuma yana sauƙaƙa damuwa.

2. Taimako da Mafita
Duk wanda ya saba yawaita wannan zikirin zai ga yadda Allah zai kawo masa mafita cikin al’amuransa.

3. Samun Albarka da Tsari
Ambaton Ya Hayyu Ya Qayyum yana kawo albarka cikin rayuwar mutum kuma yana tsare shi daga sharruka.

Misalin Addu’a Tare da “Ya Hayyu Ya Qayyum”

“Ya Hayyu Ya Qayyum, bi rahmatika astagheeth. Ya Allah, ka tsare ni daga dukkan sharruka kuma ka biyan bukatata cikin sauƙi da rahamarka.”
Wannan addu’ar za a iya yinta a kowanne lokaci, musamman cikin dare ko lokacin damuwa.


Kammalawa

Wirdin Ya Hayyu Ya Qayyum yana da sirrika masu yawa waɗanda za su taimaka wa musulmi wajen samun sauƙi da biyan bukata daga Allah. Mu yawaita wannan zikiri tare da fatan Allah zai amsa mana.

Wirdin Ya Hayyu Ya Qayyum yana da sirrika masu yawa waɗanda za su taimaka wa musulmi wajen samun sauƙi da biyan bukata daga Allah. Mu yawaita wannan zikiri tare da fatan Allah zai amsa mana.

Allah ya Kara mana dacewa Ameen