Wike Ya Kare Sanya Sunan Tinubu a Cibiyar ICC, Ya Maida Martani Ga Masu Sukan

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya kare matakin da ya ɗauka na sanya wa Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa (ICC) da ke Abuja sunan Shugaba Bola Tinubu.  Wike ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da kammala aikin hanyar gefen hagu mai tsawon kilomita 15 daga Ring Road I zuwa kwanar Wassa.

Martanin na Wike ya biyo bayan ce-ce-ku-cen da ya ɓarke a shafukan sada zumunta bayan an sanya wa cibiyar sunan shugaban ƙasa.  Wasu ‘yan Najeriya sun soki matakin, yayin da wasu kuma suka yi Allah-wadai da kashe Naira biliyan 39 da aka yi wajen gyaran ginin.

Wike ya bayyana mamakin yadda wasu ke sukar sanya sunan Tinubu a cibiyar, yana mai cewa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe ba Azikiwe ne ya gina shi ba, haka ma filin wasanni na Moshood Abiola ba Abiola ne ya gina shi ba.  Ya ƙara da cewa waɗanda ke sukar gyaran cibiyar ba su da kyakkyawan ɗanɗano wajen gane abu mai kyau.

“Na yi abin da ya dace, kuma ban yi nadama ko kaɗan ba,” in ji Wike. Ya bayyana cewa abu ɗaya tilo da bai canza ba a cibiyar shi ne ginin, yana mai cewa komai a cikin cibiyar an sauya shi.

Dangane da kuɗaɗen da aka kashe wajen gyaran, Wike ya ce waɗanda ke cewa kashe Naira biliyan 39 ba shi da muhimmanci sun manta da yadda abubuwa suka sauya da sauyin darajar Naira da Dala.  “Sun ce an gina cibiyar da Naira miliyan 240, amma a wace shekara? 1991,” in ji shi.  “To menene darajar canjin kuɗaɗe a shekarar 1991 idan aka kwatanta da yau?  Ku duba fa, 1991 aka gina ta, yanzu kuma muna cikin 2025.”

Wike ya ƙarƙare da cewa, “Babu wanda ke ƙaunar wannan ƙasa da zai soki gyaran cibiyar taron ƙasa da ƙasa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *