
Shugabar ƙaramar hukumar Egor a jihar Edo, Hon. Eghe Ogbemudia, ta yi fatali da yunkurin da wasu kansiloli suka yi na tsige ta daga kan mukamin ta. A cikin sanarwa da ta fitar, Hon. Ogbemudia ta bayyana cewa matakin da kansilolin suka ɗauka ya sabawa tsarin doka.
Ta yi zargin cewa akwai wasu jiga-jigai daga waje da suka zuga tsirarun ƴan majalisar su tsige ta domin samun damar shiga baitul malin ƙaramar hukumar. Ogbemudia ta jaddada cewa ba ta taɓa samun wata tuhuma daga ‘yan majalisar ba, kuma dukkanin matakan da suka ɗauka suna da rauni a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.
A cikin jawabin ta, ta ce, “Ni ƴar demokuraɗiyya ce kuma mai fafutukar tabbatar da bin doka da oda. Wasu tsirarun kansiloli ne suka zauna suka ce sun tsige ni, kuma ba su da wata hujja ko tanadin dokar da suka dogara da shi.”
Hon. Ogbemudia ta yi kira ga al’ummar karamar hukumar Egor da su ci gaba da bin doka da oda, tare da yin watsi da matakin da wadannan ‘yan tsirarun kansiloli suka yi. Ta kuma bayyana cewa tsige ta daga mukamin ta tare da mataimakinta ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasa.
Daga cikin labarai masu alaka, an samu rahoto daga babban kotun jihar Edo cewa an maido da shugabannin kananan hukumomi 18 da aka dakatar, wanda hakan ya ba da damar duba matakan da aka ɗauka kan shugabannin da aka tsige. Kotun ta umarci kowa ya tsaya a matsayinsa har sai ta gama sauraron karar da aka shigar gabanta, ta kuma ɗage zaman zuwa watan Fabrairu, 2025.
Wannan lamari na nuna yadda siyasa ke tafiya a jihar Edo, tare da jaddada bukatar bin doka da oda a harkokin gudanar da mulki.