
A yayin da ake shirin kakar zabe ta 2027, harkokin siyasa a Najeriya na kara daukar zafi, inda wasu ‘yan majalisar tarayya suka bayyana sauya shekarsu daga jam’iyyun da suka ci zabe a 2023 zuwa jam’iyyar APC mai mulki. A cikin shekaru biyu na mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu, akalla ‘yan majalisar tarayya tara sun fice daga jam’iyyunsu zuwa APC.
Sauya shekarsu na zuwa ne a lokacin da jam’iyyar APC ke kokarin karfafa matsayin ta a cikin siyasar Najeriya, yayin da jam’iyyar PDP ke fuskantar kalubale wajen dawo da karfinta. Wasu daga cikin ‘yan majalisar sun danganta sauya shekarsu da rikice-rikicen cikin gida da suka shafi jam’iyyun da suka bar.
Sanata Francis Onyewuchi, mai wakiltar Imo ta Gabas, ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar LP zuwa APC saboda rikice-rikicen cikin gida da suka shafi ci gaban jam’iyyar. Haka nan, Sanata Ned Nwoko daga Delta ta Arewa ya danganta sauya shekarsa da rabuwar kai a cikin PDP.
Hon. Amos Gwamna Magaji daga Kaduna, Hon. Christian Nkwonta daga Abia, da Hon. Alfred Illiya Ajang daga Jos na Kudu sun kuma bayyana dalilin sauya shekarsu a matsayin rashin jituwa a jam’iyyun su na baya.
Wasu ‘yan majalisar da suka sauya sheka sun nuna damuwarsu kan yadda rikice-rikicen jam’iyyun ke shafar ci gaban al’ummar da suke wakilta. Jam’iyyar APC na ci gaba da kokarin rage karfin ‘yan adawa, yayin da jam’iyyun hamayya ke sake tsara dabarun da zasu kwace mulki daga hannun APC.
Duk da cewa ‘yan siyasa na da ‘yancin sauya sheka, PDP ta yi Allah wadai da wannan mataki, inda ta bukaci ‘yan majalisar da suka fice da su ajiye kujerunsu bisa tanadin kundin tsarin mulki. Wannan yanayi na sauya sheka na iya shafar tasirin siyasar Najeriya a nan gaba.