Wani Matashi Ya Yi Ikirarin Zama Annabin wai ya ga Allah

A ranar Lahadi, wani matashi mai suna Qudus Ewe daga garin Saki, Jihar Oyo, ya jawo cece-kuce a Najeriya bayan ya bayyana kansa a matsayin Annabin Allah. Wannan ikirari na Qudus ya fito ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda ya ce yana ganin Allah da idonsa kuma yana magana da Shi kai tsaye.

Bayan wannan furuci, iyalan Qudus sun fito suna karyata ikirarin, suna neman gafara daga jama’a. Musulmai da dama sun bayyana bacin ransu game da wannan ikirari, wanda ya sabawa koyarwar addinin Musulunci, wanda ke nuna cewa babu wani Annabi da zai zo bayan Annabi Muhammad (SAW).

A cikin bidiyon, Qudus ya ce, “Na fi Annabi Musa girma. Na rantse da Allah. Ni Annabi ne.” Wannan ya jawo fushin al’ummar Musulmi, musamman ma a lokacin da ya ambaci Annabi Musa, wanda aka yarda da shi a matsayin daya daga cikin manyan manzanni a cikin Al-Qur’ani.

Wani malamin addinin Musulunci daga Ilorin, Sanusi Lafiagi, ya yi tsokaci kan ikirarin, yana mai cewa, “Wannan sokon shaidan ya rude shi. Ya kamata a nemo shi a tattauna da shi kafin ya jefa wasu cikin halaka da karya.”

A halin yanzu, har yanzu ba a samu karin bayani daga Qudus ko daga hukumomin addini game da wannan lamari ba, amma al’umman Najeriya suna ci gaba da tattaunawa kan wannan lamari mai tayar da hankali.