Wani Barawon Kayan Lantarki Ya Mutu Bayan Wuta Ta Kama Shi a Nsukka

Wani mutum da ake zargi da yunkurin satar wayoyin lantarki a makarantar Firamare ta Ihe, karamar hukumar Nsukka, Jihar Enugu, ya rasu bayan wuta ta kama shi. Rahotanni sun tabbatar da cewa mutumin ya zo tare da wasu abokan cin nasu, amma sun gudu bayan hadarin ya faru.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa mutumin yana kokarin cire wayoyin ƙarfe na lantarki mallakin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Enugu (EEDC) lokacin da wutar ta kama shi. Gawar mamacin ta nuna alamun ƙonewa sosai, alamar karfin wutar da ya gamu da ita.

An gano cewa mutumin ya zo tare da gungun mutane a cikin wata ƙaramar mota, amma bayan faruwar lamarin, abokan nasu sun bar shi a wurin suna tsira da rayukansu. Bincike a cikin motar da suka bar ya nuna katin shaida wanda ake zargin zai iya taimakawa wajen gano mutumin.

Wannan lamarin yana kara jaddada matsalar satar kayan lantarki a Najeriya, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin dakile irin wannan aika-aika.