
Tsohuwar Ministar Harkokin Mata a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, Uju Kennedy Ohanenye, ta kwana a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) bayan da aka tsare ta kan zargin karkatar da kudi. Wannan zargi na da alaka da kudin da aka ware domin tallafawa mata a kasafin kudin shekarar 2023.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa an karkatar da N138,413,253.89 daga kudin tallafin da aka tanada don gudanar da ayyukan da suka shafi mata. Jami’an hukumar sun yi mata tambayoyi a hedikwatar su, inda suka fara bincike kan rawar da ta taka a cikin wannan badakala.
Wata majiya daga EFCC ta bayyana cewa Uju ta isa shelkwatar hukumar da misalin karfe 11:00 na safe, inda aka fara yi mata tambayoyi dangane da zargin da ake yi mata. Wannan lamari yana daga cikin dalilan da suka jawo mata asarar kujerarta lokacin da Tinubu ya yi garanbawul a gwamnatin sa.
A cewar jaridar The Punch, zargin badakala na Uju Kennedy Ohanenye na daga cikin abubuwan da suka jawo mata matsala a lokacin mulkinta, wanda hakan ya sa aka sauke ta daga mukamin minista a watan Oktoba 2024. Tinubu ya maye gurbinta da Imaan Suleiman-Ibrahim a matsayin sabon minista.
Hukumar EFCC ta yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da bayanai kan duk wani lamari da ke da alaka da cin hanci da rashawa, tare da tabbatar da cewa suna gudanar da aikinsu na tabbatar da adalci a cikin al’umma.