
Dr. Emana Ambrose-Amawhe, tsohuwar ƴar takarar mataimakiyar gwamnan jihar Kuros Riba a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ta sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Ta tabbatar da sauya sheƙar tata ne a wani taro da aka shirya a ƙaramar hukumar Akpabuyo, inda ta bayyana cewa ci gaban da jam’iyyar APC ke samu a jihar ne ya ja hankalinta.
Dr. Emana ta ce ba ta koma APC don neman muƙami ba, sai dai don ta haɗa kai da jam’iyyar mai mulki wajen kawo ci gaba ga al’umma. Ta kuma roƙi jama’a da su ƙara haƙuri da gwamnatin APC, tana mai cewa babu wani abu mai kyau da ake samu a dare ɗaya.