
Tsohon shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara, ya bayyana damuwarsa game da halin da Arewa ke ciki. A cikin wata tattaunawa da shugabannin Kiristoci a Arewacin Najeriya, Dogara ya zargi shugabannin yankin da lalata Arewa, yana mai cewa rashin ci gaban yankin ya biyo bayan gazawarsu.
Dogara ya yi Allah wadai da yadda shugabannin Arewa suka yi watsi da ci gaban yankin a cikin shekaru 40 da suka gabata. Ya bayyana cewa, duk da cewa ana zargin cewa ‘yan kudu suna samun nadin mukamai, hakika shugabannin Arewa suna da alhakin koma bayan yankin. Ya ce, “Ya kamata a bayyana cewa Shugaba Tinubu ko Kudu ba shi ne matsalar mu ba.”
Tsohon shugaban ya shawarci ‘yan Najeriya da su daina yawan sukar gwamnatin APC da Bola Tinubu ke jagoranta, yana mai cewa ya kamata a mara wa shirye-shiryenta baya domin fitar da Najeriya daga wannan hali na talauci.
Dogara ya nemi a gyara Najeriya ta hanyar goyon bayan dokokin gyaran haraji da ke jiran amincewar majalisar dokoki. Ya bayyana cewa yana goyon bayan matakan da gwamnatin Tinubu ke dauka wajen inganta tattalin arzikin kasar, duk da kalubalen da hakan ke jawo wa.