Tsohon Shugaban Kasa, Yakubu Gowon, Ya Fadi Damuwarsa Game da Matsalar Arewa

Tsohon Shugaban Kasa, Yakubu Gowon, Ya Fadi Damuwarsa Game da Matsalar Arewa

Alhamis, Nuwamba 28, 2024
Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, ya bayyana damuwarsa game da gagarumar matsalar tsaro da shiyyar Arewa ke fuskanta. Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da tawagar tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, ta kai masa ziyara.

A cewar Gowon, rashin tsaro na kara dabaibaye yankin, wanda hakan ya sa wasu sabbin kungiyoyin ‘yan ta’adda, kamar Lakurawa, sun bayyana. Ya bayyana cewa lamarin na bukatar gaggawar kawo karshen sa domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Janar Gowon ya yi nuni da yadda ake bukatar hadin kai tsakanin al’ummomi don shawo kan matsalolin da suka addabi Arewa. Ya ce: “Duk da bambancin da ke tsakanmu, idan za mu iya hada kai ta hanyar kawar da sabanin da muke da su, za mu kawo karshen matsalolin da muke fuskanta.”

Gowon ya yaba da ziyarar da Malam Ibrahim Shekarau ya kai masa, inda ya ce hakan na nuna mutunta juna a cikin al’umma. Ya kuma bayyana fata da cewa, idan an yi aiki tare, za a iya samun hanyoyin da za a bi domin kawo karshen kalubalen tsaro da ke addabar yankin.


Wannan jawabin na Gowon ya jawo hankalin al’umma da dama, suna fatan cewa za a dauki matakan da suka dace don inganta tsaro a Arewa da sauran sassan Najeriya.