
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ci gaba da gabatar da shaidu a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tsohon ministan lantarki a gwamnatin Muhammadu Buhari, Saleh Mamman. An zarge shi da tuhuma guda 12 da suka shafi almundahanar kuɗe-kudade da suka kai kimanin Naira biliyan 33.8.
A zaman da aka yi, EFCC ta bayyana cewa Saleh Mamman ya sayi gida a birnin tarayya Abuja a kan farashin Naira miliyan 200, inda aka biya kuɗin da tsabar daloli. Shaidan da hukumar ta gabatar, Mr. Samson Bitrus, wanda ke matsayin dillalin gidaje, ya bayyana yadda ya taimaka wajen sayen gidan da tsohon ministan ya yi.
Samson ya shaidawa kotu cewa an yi cinikin ne a shekara ta 2019, inda ya tabbatar da cewa kadarar ba ta da wata matsala ta doka kafin a kammala sayan. Ya kuma bayyana cewa tsohon ministan ya zo tare da wani abokinsa yayin gudanar da cinikin.
A yayin zaman shari’ar, lauyan Saleh Mamman, Mista Femi Atteh, ya nemi kotu ta dage shari’ar domin ba shi damar yi wa shaidan tambayoyi. Wannan neman dagewa ya biyo bayan shaidar da wani mai canjin kuɗi ya bayar, wanda ya bayyana cewa bai taɓa karɓar kuɗi daga hannun wanda ake tuhuma ba, sai dai ta hannun matasan da ke zaune a gidansa.
Tuhumar Saleh Mamman na nan a gaban kotu, inda ake ci gaba da sauraron shaidun da za su taimaka wajen tantance gaskiyar lamarin. Wannan shari’a na ci gaba da jawo hankalin jama’a, yayin da ake sa ran ganin yadda za a yi maganin badakalar da aka zarge tsohon ministan.