Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Tsohon Kwamishinan Yada Labarai a Kwara Ya Rasu

Alhaji Abdulrahim Adisa, tsohon kwamishinan yada labarai a jihar Kwara, ya rasu yana da shekaru 91 a duniya. Rasuwar ta faru ne da sanyin safiyar ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba, 2024, kamar yadda kungiyar ƴan jarida (NUJ) ta tabbatar a wata sanarwa da sakataren kungiyar ya fitar.

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, yana mai addu’ar Allah ya sa shi a gidan Al-Jannah. Gwamnan ya jaddada irin gudunmawar da marigayin ya bayar a harkar yada labarai, musamman a matsayin tsohon ma’aikacin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

An gudanar da Sallar Janazar marigayi Abdulrahim Adisa da misalin karfe 10:00 na safe, inda aka birne gawarsa a makabartar musulmi da ke garin Osere a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Marigayi Abdulrahim Adisa ya rike mukamin Babban Manaja na gidan jaridar Herald mallakar gwamnatin jihar Kwara a lokacin rayuwarsa, tare da zama kwamishinan yada labarai da sadarwa. Rasuwarsa ta jawo bakin ciki ga ‘yan jarida da dama a jihar, musamman ma’aikatan jaridar Herald.