Tsohon Jami’in Gwamnatin El-Rufai Ya Fuskanci Shari’a Kan Zargin Almundahana

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gurfanar da Alhaji Bashir Sa’idu, tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kaduna a lokacin Nasir El-Rufai, a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna. Wannan mataki ya biyo bayan zargin almundahana da kuɗaɗe da aka yi masa.

An shigar da ƙarar ne a ranar Talata, 7 ga watan Janairun 2025, inda aka tuhumar Bashir Sa’idu da laifuka guda biyu na karɓar kuɗi haram, wanda hakan ya sabawa dokar hana almundahana ta shekara ta 2022.

A cikin ƙarar, an bayyana cewa a watan Maris na shekarar 2022, Bashir Sa’idu ya karɓi kuɗin haram N155,000,000 daga Ibrahim Muktar, wanda ma’aikaci ne a ma’aikatar kuɗi. Kuɗin dai an karɓe su ta hannun Muazu Abdu, wanda shi ne mataimakin sa a lokacin, wanda hakan ya sabawa doka.

Hukumar ICPC ta bayyana cewa wannan lamari ya sabawa sashe na 2(a) na dokar hana almundahana, wanda ke bayyana cewa karɓar kuɗi daga ko wane mutum ba tare da izini ba laifi ne.

Wannan lamarin ya jawo hankalin jama’a, musamman ganin cewa an riga an yi bincike na tsawon watanni 10 akan Bashir Sa’idu, wanda aka ce an wanke shi daga dukkan tuhume-tuhume a baya.

Tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya kai ziyara ga Bashir Sa’idu a gidan gyaran hali, wanda hakan ya nuna goyon bayan sa ga tsohon jami’in. Wannan ziyarar ta jawo cece-kuce a tsakanin masoya da masanan harkokin siyasa a jihar Kaduna.

A halin yanzu, ana sa ran ci gaba da sauraron shari’ar a gaban kotu, inda aka kafa kwamitin bincike kan zargin almundahana da kuɗaɗen gwamnati.