
Jihar Ondo ta rasa tsohon gwamnan soji na farko, Kyaftin Ita David Ikpeme, wanda ya rasu yana da shekaru 89 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya. Iyalansa sun tabbatar da wannan labari ga gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa a wata wasika da Iquo Ikpeme ya sanya wa hannu.
Gwamna Aiyedatiwa ya yi alhinin rasuwar marigayin, inda ya mika ta’aziyya ga iyalan Ikpeme. Ya yabawa gudunmawar da Ikpeme ya bayar wajen gina tubalin ci gaban jihar Ondo tun daga shekarar 1976 zuwa 1978, lokacin da ya zama gwamna na farko bayan kirkiro jihar daga tsohuwar jihar Yammacin Najeriya.
A cikin jawabin sa, Aiyedatiwa ya bayyana Ikpeme a matsayin jajirtaccen jagora da hazikin mai mulki, wanda ya zamo ginshiki a garinsa na haihuwa, Calabar. Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata domin ganin an yi wa marigayin jana’iza mai kyau.
Gwamnan ya yi addu’a Allah ya jiƙan marigayin, ya kuma ba iyalansa ƙarfin gwiwa da juriya. Tarihin Ikpeme zai kasance abin alfahari ga jihar Ondo da kuma al’ummar Najeriya baki ɗaya, saboda ayyukan kirki da ya yi a lokacin mulkinsa.
Daga karshe, gwamnatin jihar Ondo ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da tuna irin gudunmawar da Ikpeme ya bayar