Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Tsofaffin Ma’aikatan CBN Sun Kai Kotu Saboda Sallama da Ba Tattaunawa ba

Tsoffin ma’aikatan Babban Bankin Kasa (CBN) guda 1,000 da aka sallama daga aiki a shekarar 2024 sun shigar da karar bankin a Kotun Kwadago ta Kasa da ke Abuja. Sun zargi bankin da karya dokokin cikin gida da na kwadago kafin sallamarsu, suna mai cewa an yi hakan ne ba bisa ka’ida ba.

A cikin karar da suka shigar ranar 4 ga Yuli, 2024, tsoffin ma’aikatan sun bayyana cewa an tauye hakkinsu na kare kansu kafin a sallame su. Hakan ya sabawa dokokin aiki na CBN da na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Alkalin kotun, Mai shari’a O. A. Osaghae, ya ba da shawarar a nemi sulhu tsakanin bangarorin kafin ci gaba da shari’ar, wanda aka dage zuwa 29 ga Janairu, 2025. Tsoffin ma’aikatan suna neman kotu ta ayyana cewa sallamar da aka yi musu ba ta halatta ba, tare da umarnin dawo da su kan mukamansu da biyan su albashi da sauran alawus.

Haka zalika, suna neman diyyar Naira biliyan 30 saboda damuwa da aka jawo musu, da karin Naira miliyan 500 don biyan kudin shari’ar. CBN ya bayyana cewa ba a yi wa kowanne ma’aikaci dole ba, sannan sun ware kudade a matsayin kudin sallama.