
Trump Ya Yiwa Najeriya Barazana kan Ci Gaba da Tsare Kasurgumin Dan Ta’addan IPOB?
Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta na nuna zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump, yana neman gwamnatin Najeriya ta saki Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB.
A cikin bidiyon, an ji Trump na ba gwamnatin Najeriya wa’adin ta kwana na 31 ga Nuwamba ta saki Kanu ko ta fuskanci fushinsa. Ya kuma yi barazanar janye tallafin kiwon lafiya, kudi da na jin kai daga Najeriya, da kuma sanya takunkumi a kan kasar idan ba ta bi bukatarsa ba.
Bincike ya nuna cewa bidiyon bogi ne, an tsakuro shi ne daga jawabin nasarar Trump da ya yi bayan ya lashe zaben Amurka a ranar 6 ga Nuwambar 2024. Wa’adin da ake zargin Trump ya sanya na ranar 31 ga Nuwamba ya sanya ayar tambaya kan sahihancin bidiyon domin Nuwamba na da kwanaki 30 ne kawai. An kuma lura da kyaftawar idanuwan Trump da rashin daidaito tsakanin motsin labbansa da muryarsa wadanda suka kara zama ayar tambaya kan sahihancin bidiyon.
An gano cewa bidiyon yana amfani da fasahar kirkirar murya ta AI, wanda ke nuna cewa ba jawabin asali bane na Trump.
Nnamdi Kanu dai yana hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tun bayan da aka dawo da shi daga kasar Kenya a watan Yunin 2021 inda ake tuhumarsa da laifin cin amanar kasa.