Tinubu Ya Yi Jimamin Mutuwar Tsohon Shugaban Amurka, Jimmy Carter

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya mika ta’aziyya ga al’ummar Amurka bayan mutuwar tsohon shugaban kasar, Jimmy Carter, wanda ya rasu a ranar Lahadi bayan cika shekaru 100. Tinubu ya bayyana Carter a matsayin aboki na hakika ga Najeriya da nahiyar Afrika.

A cikin sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya jaddada irin gudummawar da Carter ya bayar wajen ci gaban al’umma. Ya ce, “Jimmy Carter mai taimakon jama’a ne, kuma fitila ta hidima ga bil’adama.”

Tinubu ya kuma tuno da yadda Carter ya jagoranci duniya wajen nuna muhimmancin taimakon jama’a, duk da barin matsayin shugaban Amurka. Ya ce, “Shugaba Carter ya nuna mana yadda za a kasance masu tasiri da amfani bayan barin matsayin shugaban Amurka.”

Najeriya ta mika ta’aziyya ga gwamnatin Amurka da al’ummarta, inda Tinubu ya bayyana fatan cewa Carter zai kasance abin tunawa ga duk masu neman ci gaban al’umma.