Tinubu Ya Yi Alkawarin Inganta Farashin Abinci a Najeriya

A yayin taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa yana aiki tukuru don inganta farashin abinci a Najeriya. Tinubu ya nuna jin dadinsa bisa saukar farashin abinci, yana mai cewa wannan yana da matukar muhimmanci, musamman da shirin watan Ramadan ke karatowa.

Tinubu ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta mai da hankali kan bunkasa harkokin abinci da zuba jari a fannonin tattalin arziki. Ya ce, “Tattalin arzikin Najeriya na kan hanyar farfadowa, kuma muna samun ci gaba a fannonin da suka shafi abinci.”

Shugaban kasar ya kuma gode wa manyan shugabannin jam’iyyar APC bisa goyon bayan da suka nuna masa. Ya bayyana cewa wannan goyon baya ya kara masa karfin gwiwa don ci gaba da kokarin inganta rayuwar al’umma.

A yayin da yake magana, Tinubu ya bayyana cewa farashin kayan abinci na raguwa, wanda ke nuni da alamar ci gaban tattalin arziki. “Najeriya tana samun cigaba yayin da sauran kasashe ke fuskantar kalubale,” in ji shi.

Shugaban kasa ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin gwamnati da su hada kai wajen inganta harkokin kasuwanci da walwalar jama’a. Ya yi alkawarin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da sauran bangarorin gwamnati don tabbatar da wadatar abinci a kasar.