
Fadar shugaban ƙasa ta yi bayani kan shirin haɗaka da ƴan adawa ke yi na zaɓen shekarar 2027, inda ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na mai da hankali ne kan inganta rayuwar ƴan Najeriya fiye da damuwa da zaɓen da ke tunkaro. Sunday Dare, mai ba da shawara na musamman ga shugaban ƙasa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X.
Dare ya ce, “Shugaba Tinubu ba ya damuwa da zaɓen 2027. Abin da ke damunsa shi ne yadda zai kawo ci gaba ga ƴan Najeriya.” Ya bayyana cewa babban burin Tinubu shi ne inganta tattalin arzikin ƙasar da kuma tabbatar da cewa manufofinsa suna haifar da sakamako mai kyau.
A halin da ake ciki, ƴan adawa suna ci gaba da shirin kafa haɗaka wanda zai ƙalubalanci Tinubu a zaɓen 2027, musamman bayan ficewar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, daga jam’iyyar APC zuwa SDP.
Sunday Dare ya kara jaddada cewa, “Muna ganin yadda asusun ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje ke ƙaruwa, da sauran alamu na ci gaba a cikin ƙasar.” Ya ce, duk da cewa akwai matsaloli, gwamnatin Tinubu na kokarin inganta rayuwar ƴan Najeriya da kuma sauya tattalin arziƙin ƙasar.
Wannan sanarwa ta fito ne a lokacin da ake ta fama da matsin tattalin arziki a ƙasar, wanda ke jawo cece-kuce a tsakanin masu ruwa da tsaki. Ana sa ran wannan yanayi zai haifar da sabbin jayayya a cikin siyasar Najeriya a cikin shekaru masu zuwa.