
A ranar Asabar, 14 ga Disamba, 2024, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa yana sane da halin matsin tattalin arziki da ƴan Najeriya ke fama da shi. A wani taron yaye ɗalibai na jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife, jihar Osun, Tinubu ya roki ƴan Najeriya su yi haƙuri da juriya a wannan lokaci mai wahala.
Shugaban ƙasan ya bayyana cewa ba da gangan ya ɗora ƴan Najeriya wahala, inda ya ce manufofinsa suna nufin gyara kura-kuran da gwamnatocin da suka gabata suka yi. Ya jaddada cewa yana son tabbatar da cewa Najeriya ta inganta ta yadda kowa zai amfana da ita.
Tinubu ya ce, “Ba na jin daɗin saka ƴan Najeriya cikin wahala, amma lokaci na bukatar mu jure raɗaɗin da ke tattare da sabbin manufofin mu.” Ya kuma bayyana cewa, duk da wahalar da ake ciki, akwai fata na samun kyakkyawar makoma idan ƴan Najeriya sun ba da haɗin kai.
A cewar Tinubu, “Muna ƙoƙarin gyara abubuwan da suka yi kuskure a baya, kuma muna kira ga ƴan Najeriya da su ba mu haɗin kai domin mu sami nasara.” Ya yi kira ga al’umma da su kasance masu juriya a wannan lokaci, yana mai tabbatar musu cewa za a sami sauƙi nan gaba.
Shugaban ƙasa ya yi magana a yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubale a fannin tattalin arziki, wanda ya shafi rayuwar al’umma da yawa. Wannan jawabi na Tinubu ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da na tattalin arziki, wanda ke nuna fatan sa na inganta halin da ƙasar ke ciki.