
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sababbin jami’an tsaron dazuka domin kare jihohin Najeriya daga hare-haren ‘yan ta’adda da miyagu. Wannan mataki na zuwa ne a cikin yanayi na karuwar hare-hare daga ‘yan bindiga da ke amfani da dazuka a matsayin mafaka.
Tinubu ya bayyana cewa za a dauki dubban matasa aiki a wannan sabon tsarin, wanda zai kasance hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi. Ma’aikatar Muhalli da Ofishin Mai ba da Shawara kan Tsaro (NSA) za su jagoranci daukar ma’aikatan da kuma tabbatar da cewa an basu horo da kayan aiki na zamani.
A cewar sanarwar da ma’aikatar muhalli ta fitar, za a raba jami’an tsaron zuwa daruruwan dazuka 1,129 da ke fadin Najeriya, domin kare su daga masu laifi. Shugaban kasa ya sha alwashin cewa ba za a bar ko yanki guda na kasar nan a hannun ‘yan ta’adda ba.
Wannan sabon shiri na daukar matasa aiki yana nufin ba su damammaki da kuma tallafa wa kokarin gwamnati na yaki da ‘yan ta’adda, tare da tabbatar da tsaron al’umma a duk fadin kasar.