Tinubu Ya Kaddamar da Sabon Tsarin Darasin Tarihi a Makarantun Najeriya

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin dawo da darasin tarihi a matsayin wajibi ga ɗaliban makarantun firamare da sakandare a Najeriya. Wannan mataki na dawo da darasin tarihi ya biyo bayan cire shi daga tsarin karatun Najeriya tun a shekarar 2007, wanda ya haifar da korafe-korafe daga al’umma.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana wannan sabuwar shawara a cikin wani shirin tashar Channels Television, inda ya ce matakin zai taimaka wa ɗalibai wajen fahimtar tarihin ƙasar domin gina al’umma mai kishin kasa. Ominasan ya ce, cire darasin tarihi daga tsarin karatun ya haifar da babban gibi a fahimtar tarihin Najeriya, musamman ga matasan ƙasar.

Tun daga shekarar 2018, gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi ƙoƙarin dawo da darasin tarihi a cikin tsarin karatun, amma ba a samu nasara ba. Tsohon ministan ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana cewa hukumar NERDC za ta tsara sabon kundin karatu mai raba tarihin daga darasin zamantakewa.

Dawo da darasin tarihi na nufin inganta ilimi da gina haɗin kai a tsakanin matasa, tare da tabbatar da cewa suna da ilimi mai zurfi game da tarihin ƙasar su. Wannan mataki na Tinubu na iya zama mai tasiri a cikin tsarin ilimi na Najeriya, da fatan zai kawo canji mai kyau ga al’umma.