
A ranar Laraba, 15 ga watan Janairu, 2025, Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta shirya tsaf domin magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar. A taron liyafa da aka gudanar a Abuja, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a yi amfani da dukkan hanyoyin da suka dace wajen ragargazar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.
Shugaban ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da samar da kayan aiki na zamani ga jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma. Tinubu ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kasance masu jarumtaka da himma, tare da inganta dabarun su na magance kalubalen tsaro.
Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa idan aka samu isassun kuɗi da kayan aiki, za a iya shawo kan matsalar ‘yan bindiga cikin kankanin lokaci. Ya kuma nuna cewa kasafin kudin ma’aikatar tsaro na bana ba ya wadatar wajen biyan bukatun sojoji da sauran ma’aikatu.
Tinubu ya yi nuni da cewa magance matsalolin tsaro na bukatar haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’ummar ƙasa. Ya ce: “Dukkan mu muna da rawar da za mu taka don tabbatar da tsaron ƙasarmu.” Shugaban ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da kula da walwala da jin daɗin jami’an tsaro, yana mai tabbatar da cewa za su sami goyon baya a duk lokacin da ake bukata.
A karshe, Shugaban ya yaba wa sojoji da sauran jami’an tsaro bisa ga sadaukarwar da suka yi wajen kare martabar ƙasa, yana mai cewa, “Sadaukarwar ku ta zama abin alfahari ga Najeriya.” Wannan jawabi na Tinubu na nuni da niyyar gwamnatin sa na tabbatar da zaman lafiya a fadin ƙasar.