
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da cewa an dage ranar gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka tsara a yi a ranar Talata, 17 ga Disamba. Sabon tsarin yanzu zai kasance a ranar Laraba, 18 ga Disamba, 2024.
Rahotanni daga majalisar dokokin Najeriya sun tabbatar da cewa wannan mataki na daga cikin shirin gyara da za a yi don inganta tsarin gabatar da kasafin. An bayyana cewa, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ne ya fara sanar da cewa Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin a ranar Talata, amma daga baya aka yi canji.
Wani babban jami’in majalisar ya bayyana cewa ana sa ran za a fitar da sanarwa a hukumance kan wannan dagewa nan ba da jimawa ba. Kafin wannan canji, an tsara taron gabatar da kasafin kuɗin Naira tiriliyan 47.9 a zauren Majalisar Wakilai tare da haɗin gwiwar Majalisar Dattawa.
Tsarin gabatar da kasafin kuɗin na shekarar 2025 yana da matuqar muhimmanci, domin zai bayyana yadda gwamnatin Tinubu za ta gudanar da kudaden gwamnati a shekara mai zuwa. Wannan kasafin zai shafi dukkanin fannonin raya kasa da kuma inganta rayuwar al’umma.
A yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan wannan lamarin, ana fatan cewa sabbin tsare-tsare da za a gabatar za su ba da damar samun tsarin da zai inganta gudanar da al’amuran gwamnati a Najeriya. Kodayake an samu jinkiri, amma ana sa ran cewa wannan sauyi zai kawo ci gaba mai ma’ana ga gwamnatin Tinubu da al’ummar Najeriya.