
A ziyarar da ya kai jihar Katsina, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi sojojin Najeriya da su zage damtse wajen kawo ƙarshen ta’addanci da sauran miyagun ayyuka a ƙasar.
Tinubu ya bayyana cewa matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta jarabawa ce, kuma yana da kwarin guiwar sojoji za su iya dawo da zaman lafiya. Ya kuma ce lokaci ya yi da za a ce “ya isa” ga ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Shugaban ƙasar ya yi wannan kiran ne ga dakarun 17 Brigade na Sojojin Najeriya da ke Katsina a ranar Juma’a. Ya bukace su da su yi amfani da gogewarsu wajen tabbatar da tsaron al’umma da dukiyoyinsu.
“Sojojinmu, ku sani wannan lokaci ne na jarabawa a tarihinmu. Barazana irin ta ta’addanci da ‘yan bindiga sun shafe tsawon lokaci suna damun mu,” in ji Tinubu. “Yanzu lokaci ya yi da za mu ce ya ishe su.”
Ya ƙara da cewa, “Ina so muryar saƙonku ta karade dazuka da duwatsu, ku shaida wa makiyan Najeriya cewa lokaci ya kure musu.”