
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana kan muhimmin ci gaban da aka samu a matatar Warri a jihar Delta, inda aka fara aikin gyaranta a ranar Litinin. Wannan mataki ya faranta ran shugaban kasa, wanda ya yaba wa kamfanin NNPCL bisa wannan nasara.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya bayyana cewa farawa da aikin matatar Warri na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasar. Ya ce wannan nasara za ta karfafa gwiwar ‘yan Najeriya kan alƙawarin gwamnatin sa na samar da ingantaccen makamashi.
Bayan yabon ga aikin da aka gudanar, Tinubu ya kuma yi kira ga kamfanin NNPCL da ya ƙara mai da hankali kan gyaran matatar Kaduna. Ya bayyana cewa gyaran wannan matatar zai tabbatar da matsayin Najeriya a fannin samar da makamashi a duniya.
“Matatar Kaduna tana da muhimmanci ga kasar, kuma ina fatan kamfanin NNPCL zai mai da hankali wajen ganin an kammala aikin cikin gaggawa,” in ji Tinubu.
Shugaban ya jaddada cewa dawo da dukkanin matatun Najeriya guda huɗu ya na da matukar muhimmanci wajen mayar da Najeriya cibiyar tace ɗanyen man fetur a Afirka. Wannan kira na Tinubu na zuwa ne a lokacin da kasar ke fuskantar kalubale a fannin samar da makamashi.