Tinubu Ya Bayyana Matakan Da Ya Dauka Domin Tabbatar Da Ci Gaban Tattalin Arzikin Najeriya

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta dade tana fuskantar matsalolin tattalin arziki, wanda hakan ya jawo kashe kudin ‘yan kasa da za a haifa a gaba. A yayin taron da ya gudanar da tsofaffin ‘yan majalisar dokoki na Jamhuriyya ta Uku a fadar gwamnati, Tinubu ya ce matakan da gwamnatinsa ta ɗauka sun hana tattalin arzikin ƙasar durƙushewa.

Tinubu ya bayyana cewa, “Mun fuskanci manyan matsaloli a lokacin da muka karɓi mulki. Idan ba mu ɗauki matakan da muka ɗauka ba, da yanzu bashi ya yi wa Najeriya katutu.” Ya kuma jaddada cewa an fara ganin canje-canje a cikin tattalin arzikin ƙasar, inda darajar Naira ke fara daidaita, sannan farashin kayayyaki na raguwa.

Shugaban ƙasar ya gode wa ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suka bayar kan matakan tattalin arzikin da ya ɗauka. Haka zalika, ya ce jajircewa a kan tafarkin dimokuradiyya ce hanya mafi dacewa da za ta kawo ci gaba a ƙasar.

A cikin wannan taron, tsohon sanata Emmanuel Chiedoziem Nwaka ya yaba da shirye-shiryen tallafin karatu da na basussuka da gwamnatinsa ta bayar, yana mai cewa wannan yana taimakawa matasa wajen samun damar samun rance don sayen motoci ko gidaje ba tare da sun tara dukiya ba.

Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ware miliyoyin talakawa don tallafa musu, wanda hakan ke nuna kokarin gwamnatin wajen inganta rayuwar ‘yan kasa. Wannan mataki na Tinubu na nuna alamar kyakkyawan fata ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya a nan gaba.