Tinubu Ya Bayyana Hanyoyin Inganta Tattalin Arzikin Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa canje-canjen tattalin arzikin da gwamnatin sa ta aiwatar suna samun sakamako mai kyau a Najeriya. A yayin tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar, Tinubu ya jaddada cewa wannan ci gaban ya jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje, ciki har da kamfanonin mai na duniya.

Shugaban ya yi kira ga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da ta hada kai da Najeriya wajen inganta harkokin kasuwanci da zuba jari a fannin tattalin arziki. Ya bayyana cewa an fara ganin sakamakon manufofin da gwamnatinsa ta dauka, duk da cewa rahoton hukumar kididdiga na kasa ya nuna an samu hauhawar farashi a kasuwa.

Tinubu ya bayyana cewa yana fatan ci gaban tattalin arzikin Najeriya zai kara karfafa alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da UAE. Har ila yau, ya nemi gwamnatin UAE da ta zuba jari a Najeriya domin inganta tattalin arzikin kasar.

A yayin ziyarar da yayi a kasar UAE, Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa na fatan shawo kan kalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, tare da inganta hadin kai tsakanin kasashen biyu.

Wannan jawabi na Tinubu na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar kalubale a fannin tsaro da tattalin arziki, inda ake fargabar tasirin hauhawar farashi a kasuwannin kayayyaki. Jami’an gwamnati sun bayyana cewa zuba jari daga kasashen waje zai taimaka wajen rage wannan matsala da kuma inganta rayuwar al’umma.