Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Tinubu Na Neman Goyon Bayan Manyan Arewa Kan Kudirin Gyaran Haraji

Shugaba Bola Tinubu ya fara tura wakilai zuwa wurin manyan Arewa domin samun goyon baya kan sabbin kudirin gyaran haraji da gwamnatin sa ta gabatar. Duk da haka, gwamnonin Arewa sun jaddada matsayinsu na kin amincewa da wannan kudiri.

Shugaban gwamnonin Arewa, Gwamna Muhammad Yahaya, ya ce ba za su janye matsayinsu ba har sai an sake nazarin kudirin gyaran harajin. A cewar wani jami’in gwamnati, Tinubu na amfani da hanyoyi daban-daban don tabbatar da an gyara muhimman bangarorin kudirin, yayin da yake tuntubar wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar Arewa.

Wannan mataki na Tinubu ya biyo bayan jaddada matsayar gwamnonin Arewa na kin amincewa da kudirin gyaran haraji, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin al’umma. Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta kuma bukaci Tinubu da ya janye kudurorin gyaran haraji da ya gabatarwa majalisa, suna zargin gwamnatin sa da yin kama-karya wajen tsara kudurorin.

Gwamnan Gombe, Muhammad Yahaya, ya tabbatar da cewa gwamnonin Arewa suna nan kan matsayinsu na kin amincewa, suna mai cewa wannan matsayar ba ta sauya ba. Hakan na nuni da cewa akwai bukatar a tattauna a kan wannan kudiri kafin a yanke hukunci na karshe.